Amma kuma Inter Miami ta Amurka sa ran janye Messin
Sa'o'i 2 da suka wuce
Kungiyar Al Hilal ta Saudiyya, ta yi wa Messi tayin ba shi albashin da ya fi na kowa ne dan bal a duniya. (Mirror)
To amma kuma kungiyar Inter Miami ta gasar Amurka na sa ran sayen dan wasan da kuma Sergio Busquets, na Barcelona a kaka mai zuwa. (Sport - in Spanish)
Chelsea ta yi wa dan wasanta na tsakiya Mason Mount farashin fam miliyan 70 duk da cewa dan Ingilan na cikin shekarar karshe ta kwantiraginsa a kungiyar. (Athletic)
Shi dai Mount yana sha'awar tafiya Bayern Munich, domin ya sake hadewa da tsohon kociyansa a Chelsea Thomas Tuchel. (Guardian).
Haka kuma zakarun na Jamus, Bayern Munich na dab da kammala yarjejeniya da mataimakin kociyan Chelsea Anthony Barry, dan Ingila. (90min)
Dan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice, a yanzu ba shi ne wanda Bayern ke matukar so ba, kuma kungiyar ta musanta cewa ta tattauna da wakilan dan wasan a makon da ya gabata. (Sky Sports)
Har yanzu Harry Kane ne dan wasan da Manchester United ta fi so a neman dan gaban da take yi.
Amma kuma matashin dan wasan Ajax da Ghana Mohammed Kudus, da kuma dan gaban Benfica da Portugal Goncalo Ramos, na daga cikin wadanda take hari idan ta rasa Kane. (Manchester Evening News)
Fatan Manchester United na sayen Frenkie de Jong, na Holland ka iya samun tagomashi daga zawarcin da Barcelona ke yi na Ilkay Gundogan na Manchester City. (Mirror)
Wakilin Gundogan ya musanta cewa kyaftin din na Manchester City ya yanke shawara kan makomarsa yana mai cewa korafsa a bude take har yanzu ga mai bukata. (Guardian)
Mai yuwuwa West Ham ta rabu da kociyanta David Moyes a karshen kakar nan ko da kungiyar ta kauce wa faduwa adaga Premier. (90min)
Watakila Leeds United ta yi zawarcin tsohon kociyan Crystal Palace, Patrick Vieira, a bazara idan Javi Gracia da aka nada ya gaji Jesse Marsch ya ki tsayawa. (TalkSPORT)
Dan wasan baya na Manchester City Aymeric Laporte, dan Sifaniya shi ne wanda Paris St-Germain ta fi so a yanzu. (Football Insider)
Chelsea da Tottenham za su yi gogayya wajen zawarcin dan bayan Inter Milan da Italiya Alessandro Bastoni, a bazara. (Fichajes)
Matashin dan gaban Brighton dan Jamhuriyar Ireland Evan Ferguson mai shekara 18 na son ci gaba da zama a kungiyar duk da sha'awarsa da kungiyoyin Premier da yawa ke yi. (Sun)
Kungiyoyin Premier da dama na son dan bayan Barcelona dan Denmark Andreas Christensen. (ESPN)
Ansu Fati na son ci gaba da zama a Barcelona duk da cewa ba a sa shi wasa sosai a kungiyar. (AS)
David de Gea, ya ce yana jin dadin zamansa a Manchester United yayin da kungiyar ke tattaunawa da shi kan sabon kwantiragi. (Sky Sports)
Dan gaban Leeds United da Sifaniya ka iya barin kungiyar da bazara idan ta fadi daga Premier. (Football Insider)
Olivier Giroud, na shirin kulla sabuwar yarjejeniya da AC Milan, wadda za ta kai har zuwa 2024. (Fabrizio Romano)
An yi wa AC Milan tayin dan wasan Guinea Naby Keita, kafin karewar kwantiraginsa a Liverpool a bazara. (Calciomercato)
Jose Mourinho ya ce yana son ci gaba da zama a kungiyar kamar yadda kwantiraginsa ya tanada zuwa 2024.
Ana rade-radin cewa kociyan dan Portugal zai bar kungiyar domin ya koma Paris St-Germain. (Corriere dello Sport)


0 Comments