Wani abin tausayi da zai iya sanya hawaye ko kuka shi ne, cin karo da yarinyar da bai kamata a ce an ganta airin wannan wuri ba, wannan ya hada kankantar shekaru,
Da kuma yunkurin ganin sai kwatanta abin da na gaba dai ta ke yi, mafi muni shi ne, wadanda suke da halayya ta neman mata, ko kuma mazinata su ne ke ta kokarin ganin sun kusance ta.Wakilinmu ya ce ya taba ganin yarinyar da duka-duka shekarunta ba su haura 12 zuwa 23 ba wacca saboda kankantarta ma in ban da aiken ta ba a bin da ake iya yi, amma wasu kuma kullum bukatarsu su ga sun kawar da ita.
Ba wannan ne ya bani mamaki ba, yadda a wasu lokutan za ka ga tana rike da karan taba sigari a hannunta tana zuka, hakan na nuni da ita ma ta fara hawa kan turba kenan.
Wani babban abin tausayi da ya gani a mazowa gidan domin aiwatar da sana’arsu shi ne, ganin masu manyan shekaru daga sashen wasu mata da har yanzu basu san Annabi ya faku ba a gidan suna zuwa kallon yadda yara matasa ke cashewa madadin su tub asu koma ga Allah.


0 Comments